Ezekiyel 46:13-15
13
“ ‘Kullum za ku tanada ɗan rago bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji; kowace safiya za ku tanada shi.
14
Tare da shi za ku tanada hadaya ta gari kowace safiya, da ya haɗa da kashi ɗaya bisa shida na efa tare da kashi ɗaya bisa uku na mai ga garin da aka cuɗa. Miƙawar wannan hadaya ta gari ga Ubangiji dawwammamiyar farilla ce.
15
Saboda haka za a tanada ɗan rago da hadaya ta gari da kuma mai kowace safiya don hadaya ta ƙonawa ta kullum.
Settings