Skip to content
Ezekiyel 46:1-8

Ezekiyel 46:1-8

1
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a rufe ƙofa ta fili na can cikin da take fuskantar gabas ranaku shida na aiki, amma a ranar Asabbaci da kuma a ranar ganin Sabuwar Wata a buɗe ta.
2
Sarki zai shiga daga waje ta shirayin hanyar shiga yă tsaya a madogarar ƙofa. Firistoci za su miƙa hadayarsa ta ƙonawa da hadayunsa na salama. Zai yi sujada a madogarar ƙofar hanyar shiga sa’an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da yamma.
3
A Asabbatai da kuma a Sabuwar Wata mutanen ƙasar za su yi sujada a gaban Ubangiji a mashigin wannan hanyar shiga.
4
Hadaya ta ƙonawar da sarki ya kawo wa Ubangiji a ranar Asabbaci ’yan raguna shida ne da rago guda, dukansu marasa lahani.
5
Hadayar garin da aka bayar tare da ragon efa guda ne, hadayar garin da ’yan ragunan yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa.
6
A ranar Sabuwar Wata zai miƙa ɗan bijimi, ’yan raguna guda shida da kuma rago guda, dukansu marasa lahani.
7
Zai tanada a matsayin hadaya ta gari, efa guda tare da bijimi, efa guda tare da ’yan raguna, da kuma ’yan raguna yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa.
8
Sa’ad da sarki zai shiga, zai shiga ta shirayin hanyar shiga, zai kuma fita ta nan.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options