Skip to content
Ezekiyel 45:21-24

Ezekiyel 45:21-24

21
“ ‘A wata na fari a rana ta goma sha huɗu za ku kiyaye Bikin Ƙetarewa, bikin da yakan ɗauki kwana bakwai, a lokacin ne za ku riƙa cin burodi marar yisti.
22
A wannan rana sarki zai tanada bijimi a matsayin hadaya don zunubi domin kansa da kuma domin dukan mutanen ƙasar.
23
Kowace rana a kwanaki bakwai na Bikin zai tanada bijimai guda bakwai da raguna bakwai marar lahani a matsayi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da kuma bunsuru saboda hadaya don zunubi.
24
Zai tanada efa na gari don kowane bijimi da kuma efa don kowane rago, tare da kwalabar mai don kowane efa guda.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options