Ezekiyel 44:9
Ana nuna aya 9 tare da mahallin da ke kewaye.
6
Faɗa wa ’yan tawayen gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ayyukan banƙyamarku sun isa haka, ya gidan Isra’ila!
7
Ban da dukan sauran ayyukanku na banƙyama, kun kawo baƙi marasa kaciya a zuciya da jiki a wurina mai tsarki, kun kuma ƙazantar da haikalina yayinda kuke miƙa mini abinci, kitse da kuma jini, kun kuma karya alkawarina.
8
A maimakon yin ayyukanku bisa ga abubuwana masu tsarki, kun sa waɗansu su lura da wurina mai tsarki.
9
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba baƙo marar kaciya a zuciya da jiki da zai shiga wurina mai tsarki, kai, har ma da baƙin da suke zama a cikin Isra’ila.
10
“ ‘Lawiyawan da suka yi nesa da ni sa’ad da Isra’ila suka kauce da kuma waɗanda suka karkata daga gare ni suka bi gumakansu, dole su ɗauki alhakin zunubinsu.
11
Za su iya yin hidima a wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin haikali suna kuma hidima a cikinsu; za su iya yankan hadayun ƙonawa da sadaka don mutane su kuma tsaya a gaban mutane su yi musu hidima.
12
Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Settings