Ezekiyel 36:8
Ana nuna aya 8 tare da mahallin da ke kewaye.
5
ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa cikin kishina mai ƙuna na yi magana gāba da sauran al’ummai, da kuma gāba da Edom, gama da farin ciki da reni a zukatansu suka mai da ƙasata mallakarsu don su washe wuraren kiwonta.’
6
Saboda haka ka yi annabci game da ƙasar Isra’ila ka kuma ce wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al’ummai.
7
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa na ɗaga hannuna sama na rantse cewa al’ummai da suke kewaye da ku za su sha ba’a.
8
“ ‘Amma ku, ya duwatsun Isra’ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanena Isra’ila, gama ba da daɗewa ba za su komo gida.
9
Na damu da ku kuma zan dube ku da tausayi; za ku nome ku kuma shuka,
10
zan kuma riɓaɓɓanya mutane a kanku, dukan gidan Isra’ila ke nan. Za a zauna a birane a kuma sāke gina rusassun wurare.
11
Zan sa mutane da dabbobi su yi yawa a kanku, za su kuma ba da ’ya’ya su kuma yi yawa. Zan zaunar da mutane a kanku kamar dā zan kuma sa ku wadaita fiye da dā. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
Settings