Ezekiyel 36:24-38
24
“ ‘Gama zan fitar da ku daga al’ummai; zan tattara ku daga dukan ƙasashe in komo da ku zuwa ƙasarku.
25
Zan yayyafa muku ruwa mai tsabta, zan kuwa tsarkake ku daga dukan ƙazantarku daga kuma dukan gumakanku.
26
Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama.
27
Zan kuma sa Ruhuna a cikinku in kuma motsa ku ku bi ƙa’idodina ku kuma kiyaye dokokina.
28
Za ku zauna a ƙasar da na ba wa kakanninku; za ku zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku.
29
Zan cece ku daga dukan rashin tsabtarku. Zan sa hatsi ya yi yalwa ba zan kawo yunwa a kanku ba.
30
Zan ƙara ’ya’yan itatuwa da amfanin gona, saboda kada ku ƙara shan kunya a cikin al’ummai saboda yunwa.
31
Sa’an nan za ku tuna mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda zunubanku da kuma ayyukanku na banƙyama.
32
Ina so ku san cewa ba na yi wannan saboda ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku ji kunya ku kuma giggita saboda halinku, ya gidan Isra’ila!
33
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na tsarkake ku daga dukan zunubanku, zan sāke zaunar da ku a garuruwanku, a kuma sāke gina kufai.
34
Ƙasar da take kango a dā za ku nome ta a maimakon zama kango a idon dukan masu ratsawa a cikinta.
35
Za su ce, “Wannan ƙasar da take kango a dā ta zama kamar lambu Eden; biranen da dā suke kufai, kango da kuma aka lalata, yanzu suna da katanga ana kuma zama a ciki.”
36
Sa’an nan al’ummai kewaye da ku da suka rage za su san cewa Ni Ubangiji na sāke gina abin da aka lalace na kuma sāke shuka abin da yake kango. Ni Ubangiji na faɗa, kuma zan aikata.’
37
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa har yanzu zan ji roƙon gidan Isra’ila in kuma yi musu wannan. Zan sa mutanensu su yi yawa kamar tumaki,
38
yawansu ya yi kamar garken tumaki don hadaya a Urushalima a ƙayyadaddun lokuta bukukkuwarta. Haka biranen da suke kufai za su cika da ɗumbun mutane. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
Settings