Skip to content
Ezekiyel 36:1

Ezekiyel 36:1

Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
“Ɗan mutum, ka yi annabci wa duwatsun Isra’ila ka ce, ‘Ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji.
2
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa abokin gāba yana magana game da ku cewa, “Yauwa! Tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu.” ’
3
Saboda haka ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin sun lalace ku suka kuma maishe ku kufai marar amfani a kowane gefe saboda ku zama mallakar sauran al’ummai da kuma abin magana da tsegumi ga mutane,
4
saboda haka, ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana faɗa wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, wa kufai da garuruwan da suka zama kango waɗanda aka washe aka wulaƙanta suka zama ganimar sauran al’ummai da suke kewaye da ku,
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 90 chars

Options