Skip to content
Ezekiyel 34:10-16

Ezekiyel 34:10-16

10
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da makiyaya kuma zan nemi hakkin tumakina daga gare su. Zan hana su yin kiwon tumakin don kada makiyayan su ƙara yin kiwon kansu. Zan ƙwace tumakina daga bakunansu, ba kuwa za su ƙara zama abincinsu.
11
“ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan nemi tumakina.
12
Kamar yadda makiyayi yakan lura da tumakinsa da suka watse sa’ad da yake tare da su, haka zan lura da tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.
13
Zan dawo da su daga al’ummai in kuma tattara su daga ƙasashe, zan kuma kawo su cikin ƙasarsu. Zan yi kiwonsu a kan duwatsun Isra’ila, a maɓulɓulai da kuma cikin wuraren zamansu a ƙasar.
14
Zan kula da su a wurin kiwo mai kyau, kuma ƙwanƙolin duwatsun Isra’ila ne zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, a can kuma za su yi kiwo a wurin kiwo mai kyau a kan duwatsun Isra’ila.
15
Ni kaina zan lura da tumakina in kuma sa su kwanta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
16
Zan nemi ɓatattuna in kuma dawo da waɗanda suka yi makuwa. Zan ɗaura raunin waɗanda suka ji ciwo in kuma ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafa da kuma masu ƙiba. Zan yi kiwo tumaki da adalci.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options