Skip to content
Ezekiyel 32:22-26

Ezekiyel 32:22-26

22
“Assuriya tana can tare da dukan sojojinta; an kewaye ta da kaburburan dukan waɗanda aka kashe, dukan waɗanda suka mutu ta wurin takobi.
23
Kaburburansu suna cikin zurfafan rami kuma sojojinta suna kwance kewaye da kabarinta. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun mutu, an kashe su da takobi.
24
“Elam tana can, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu sun mutu, an kashe su da takobi. Dukan waɗanda suka haddasa tsoro a ƙasar masu rai sun gangara wurin marasa kaciya a duniyar da take ƙarƙashi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
25
An yi mata gado a cikin matattu, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi. Domin tsoronsu ya bazu cikin ƙasar masu rai, suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami; an kwantar da su tare da waɗanda aka kashe.
26
“Meshek da Tubal suna can, tare da dukan jama’arsu kewaye da kaburburansu. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi domin sun haddasa tsoronsu a ƙasar masu rai.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options