Ezekiyel 31:3-6
3
Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi; ya yi tsayi ainun kansa ya kai cikin gizagizai.
4
Ruwa ya sa ya yi girma, zurfafan maɓulɓulai sun sa ya yi tsayi; rafuffuka suna gudu kewaye da tushensa yana aika da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi.
5
Saboda haka ya yi tsayi fiye da sauran itatuwan kurmi; rassansa suka ƙaru suka yi tsayi, suka bazu saboda yalwar ruwaye.
6
Dukan tsuntsayen sararin sama suka yi sheƙa a rassansa, dukan namun jeji suka haihu a ƙarƙashin rassansa; dukan al’ummai suka zauna a inuwarsa.
Settings