Skip to content
Ezekiyel 30:1-8

Ezekiyel 30:1-8

1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Yi kuka kana cewa, “Kaito saboda wannan rana!”
3
Gama ranar ta yi kusa, ranar Ubangiji ta gabato, ranar gizagizai, lokacin hallaka wa al’ummai.
4
Takobi zai zo a kan Masar, azaba za tă zo a kan Kush. Sa’ad da kisassu za su fāɗi a Masar, za a kwashe dukiyarta a tafi a rushe harsashinta.
5
Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.
6
“ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Daga Migdol zuwa Aswan za su mutu ta wurin takobi a cikinta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
7
Za su zama kango a cikin ƙasashen da suke kango, biranensu kuwa za su zama kufai a cikin biranen da suka lalace.
8
Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da suka ga na sa wuta wa Masar aka kuma ragargaza masu taimakonta.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options