Skip to content
Ezekiyel 30:10-19

Ezekiyel 30:10-19

10
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan kawo ƙarshen mutanen Masar ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babilon.
11
Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai, za a kawo don su hallaka ƙasar. Za su zāre takuba a kan Masar su kuma cika ƙasar da kisassu.
12
Zan kafe rafuffukan Nilu in sayar da ƙasar ga mugayen mutane; ta hannun baƙi zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta. Ni Ubangiji na faɗa.
13
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.
14
Zan lalace Masar ta Bisa in ƙuna wuta wa Zowan in zartar da hukunci a kan Tebes.
15
Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum, kagarar Masar, in kuma datse mutanen Tebes.
16
Zan ƙuna wuta wa Masar; Felusiyum za tă sha azaba mai zafi. Za a tayar wa Tebes da hankali; Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai.
17
Samarin Heliyofolis da Bubastis za su mutu ta wurin takobi, biranen kansu za su tafi bauta.
18
Duhu ne zai zama rana a Tafanes sa’ad da na karye ikon Masar; a can ƙarfin da take fariya zai ƙare. Za a rufe ta da gizagizai ƙauyukanta kuma za su tafi bauta.
19
Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options