Skip to content
Ezekiyel 26:7-14

Ezekiyel 26:7-14

7
“Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa daga arewa zan kawo wa Taya Nebukadnezzar sarkin Babilon, sarkin sarakuna, tare da dawakai da kekunan yaƙi, da mahayan dawakai da babbar rundunar soja.
8
Zai kashe mazaunan filin ƙasar da takobi; zai yi miki ƙawanya, ya gina miki mahaurai, sa’an nan ya rufe ki da garkuwoyi.
9
Zai rushe katangarki da dundurusai, ya rurrushe hasumiyoyinki da makamai.
10
Dawakansa za su yi yawa har su rufe ke da ƙura. Katanga za su girgiza saboda motsin dawakan yaƙi, kekunan doki da keken yaƙin sa’ad da suka shiga birnin da aka rushe katangar.
11
Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki; zai kashe mutanenki da takobi, ginshiƙanki masu ƙarfi kuma za su fāɗi a ƙasa.
12
Za su washe dukiyarki, kayan cinikinki kuma su zama ganima; za su rurrushe katangarki su ragargaza gidajenki masu kyau su kuma zubar da duwatsunki, katakanki da kuma tarkacenki a cikin teku.
13
Zan kawo ƙarshen waƙoƙinki masu surutu, ba kuwa za a ƙara jin kaɗe-kaɗen garayunki ba.
14
Zan maishe ki fā, za ki kuma zama wurin shanya abin kamun kifi. Ba za a sāke gina ki ba, gama Ni Ubangiji na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options