Ezekiyel 26:17-18
17
Sa’an nan za su yi makoki game da ke su ce, “ ‘Yaya kika hallaka haka nan, ya birnin da ta yi suna, cike da mutanen teku! Ke da kika zama mai ƙarfi cikin tekuna, ke da mazauna cikinki; kin sa tsoronki a kan dukan waɗanda suka zauna a can.
18
Yanzu tsibirai suna rawar jiki a ranar fāɗuwarki; tsibirai a cikin teku sun tsorata a ɓacewarki.’
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.