Ezekiyel 25:1
Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa ka kuma yi annabci a kansu.
3
Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun ce “Yauwa” a kan wuri mai tsarkina sa’ad da aka ƙazantar da shi da kuma a kan ƙasar Isra’ila sa’ad da aka mai da ita kufai da lokacin da aka kai mutanen Yahuda bautar talala,
4
saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku.
Settings