Skip to content
Ezekiyel 23:36-44

Ezekiyel 23:36-44

36
Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, za ka shari’anta Ohola da Oholiba? To, sai ka kalubalance su da ayyukansu masu banƙyama,
37
gama sun yi zina kuma jinin yana a hannuwansu. Sun yi zina da gumakansu; har suka miƙa ’ya’yansu da suka haifa mini, su zama musu abinci.
38
Sun kuma yi mini wannan. A lokaci guda sun ƙazantar da wuri mai tsarkina suka ɓata Asabbataina.
39
A ranar da suka miƙa ’ya’yansu ga gumakansu, sai suka shiga wuri mai tsarkina suka kuma ƙazantar da shi. Abin da suka yi a gidana ke nan.
40
“Sun ma aiki manzanni wa mutanen da suka zo daga nesa, kuma da suka iso kun yi wanka dominsu, kuka yi shafe-shafen idanunku, kuka kuma sa kayan adonku.
41
Kuka zauna a gado mai daraja, da tebur a shirye a gabanku wanda kun ajiye turare da maina.
42
“Surutun taron mutane marasa kula suna kewaye da ita; aka kawo Sabenawa daga hamada tare da mutane daga mashaya, suka sa mundaye a hannuwan macen da kuma ’yar’uwarta suka kuma sa rawani masu kyau a kawunansu.
43
Sai na yi magana a kan wadda ta ƙare ƙarfi ta wurin karuwanci na ce, ‘Yanzu bari su yi amfani da ita kamar karuwa, gama abin da take ke nan.’
44
Suka kuwa kwana da ita. Kamar yadda maza suke kwana ta karuwa, haka suka kwana da waɗannan lalatattun mata, Ohola da Oholiba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options