Ezekiyel 22:25-28
25
Akwai haɗin bakin sarakunanki a cikinki kamar rurin zaki mai yayyage ganimarsa; suna cin mutane, suna kwashe dukiya da abubuwa masu daraja suna mai da yawanci gwauraye a cikinki.
26
Firistocinki suna karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana; ba sa bambanta tsakanin tsarki da marar tsarki; suna koyarwa cewa babu bambanci tsakanin marar tsarki da mai tsarki; suna kuma rufe idanunsu ga kiyaye Asabbataina, da haka suke saɓon sunana.
27
Shugabanninki a cikinki suna kama da kyarketai masu yayyage ganimarsu; suna kisa suna kuma kashe mutane don samun ƙazamar riba.
28
Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba.
Settings