Ezekiyel 21:28
Ana nuna aya 28 tare da mahallin da ke kewaye.
25
“ ‘Ya kai ƙazantaccen mugu, yerima Isra’ila, wanda kwanansa ta zo, wanda lokacin hukuncinsa ya cika fal,
26
ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka kunce rawanin, ka ɗauke rawanin nan. Ba zai zama kamar yadda yake ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da mai girma.
27
Hallaka! Hallaka! Zan hallaka shi! Ba za a maido da shi ba sai ya ga ainihin mai shi; gare shi zan bayar da shi.’
28
“Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu. “ ‘Takobi, takobi, an ja don kisa, an goge don cinyewa yana haske kamar walƙiya!
29
Duk da wahayin ƙarya game da kai, duban ƙarya game da kai, za a sa shi a wuyan mugaye waɗanda za a kashe, waɗanda kwanansu ta zo, waɗanda lokacin hukuncinsu ya cika fal.
30
“ ‘Ka mai da takobi a kubensa. A inda aka halicce ka, a ƙasar kakanninka, zan hukunta ka.
31
Zan zub da hasalata a kanka in hura maka wutar fushina; Zan ba da kai a hannun mugayen mutanen da suka gwanince a hallakarwa.
Settings