Ezekiyel 13:10-11
10
“ ‘Domin sun ɓad da mutanena, suna cewa, “Salama,” sa’ad da ba salama, kuma saboda, sa’ad da ana gina katanga marar ƙarfi, sukan shafe ta da farar ƙasa,
11
saboda haka ka faɗa wa waɗanda suka shafe da farar ƙasa cewa za tă fāɗi. Ruwan sama zai sauko da rigyawa, zan kuma aika da ƙanƙara, kuma babbar iska za tă ɓarke.
Settings