Fitowa 35:3
Ana nuna aya 3 tare da mahallin da ke kewaye.
1
Musa ya tara dukan jama’ar Isra’ilawa ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku, ku yi.
2
Kwana shida za ku yi aiki, amma rana ta bakwai za tă zama rana mai tsarki, Asabbaci ne na hutu ga Ubangiji. Duk wanda ya yi aiki a wannan rana dole a kashe shi.
3
Kada ku hura wuta a cikin duk mazauninku a ranar Asabbaci.”
4
Musa ya ce wa dukan jama’ar Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.
5
Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla;
6
shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya;
Settings