Skip to content
Fitowa 30:1-6

Fitowa 30:1-6

1
“Ka yi bagade da itacen ƙirya don ƙona turare.
2
Zai zama murabba’i, tsawon zai zama kamu ɗaya, fāɗi kuma kamu ɗaya, amma tsayin yă zama kamu biyu, ƙahoninsa kuma su zama ɗaya da shi.
3
Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.
4
Ka yi zobai biyu na zinariya domin bagade a ƙarƙashin zubin, biyu a gefe da gefe su fuskanci juna, don su riƙe sandunan da ake amfani da su don ɗaukarsa.
5
Ka yi sandunan nan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.
6
Ka sa bagaden a gaban labulen da yake gaban akwatin alkawari, a gaba murfin kafara wanda yake bisa akwatin alkawari, inda zan sadu da kai.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options