Skip to content
Fitowa 30:1-15

Fitowa 30:1-15

1
“Ka yi bagade da itacen ƙirya don ƙona turare.
2
Zai zama murabba’i, tsawon zai zama kamu ɗaya, fāɗi kuma kamu ɗaya, amma tsayin yă zama kamu biyu, ƙahoninsa kuma su zama ɗaya da shi.
3
Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.
4
Ka yi zobai biyu na zinariya domin bagade a ƙarƙashin zubin, biyu a gefe da gefe su fuskanci juna, don su riƙe sandunan da ake amfani da su don ɗaukarsa.
5
Ka yi sandunan nan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.
6
Ka sa bagaden a gaban labulen da yake gaban akwatin alkawari, a gaba murfin kafara wanda yake bisa akwatin alkawari, inda zan sadu da kai.
7
“Haruna zai ƙone turare a bisa bagaden kowace safiya, sa’ad da yake shirya fitilu.
8
Dole Haruna yă ƙone turare sa’ad da ya ƙuna fitilu da yamma, ta haka za a riƙa ƙona turare a gaban Ubangiji, daga tsara zuwa tsara.
9
Ba za a ƙona wani irin turare dabam a bisa wannan bagade ba, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta hatsi, ko ta sha a bisansa ba.
10
Sau ɗaya a shekara, Haruna zai yi kafara a bisa ƙahoninsa. Dole a yi wannan kafara ta shekara-shekara da jinin kafara ta hadaya don zunubi daga tsara zuwa tsara. Gama bagaden mafi tsarki ne ga Ubangiji.”
11
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
12
“Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su.
13
Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji.
14
Duk waɗanda suka ƙetare, waɗanda shekarunsu ya kai ashirin ko fiye, za su ba da hadaya ga Ubangiji.
15
Masu arziki ba za su bayar fiye da rabin shekel ba, talakawa kuma ba za su bayar ƙasa da haka ba, sa’ad da za ku yi hadaya ga Ubangiji don kafara rayukanku.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options