Skip to content
Fitowa 29:38-46

Fitowa 29:38-46

38
“Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya.
39
Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma.
40
Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.
41
Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
42
“Wannan za tă zama hadaya ta ƙonawar da za a dinga yi kowace rana, daga tsara zuwa tsara. Za a yi ta miƙa hadayar a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. A can zan sadu da kai, in yi magana da kai;
43
a can kuma zan sadu da Isra’ilawa, in kuma tsarkake wurin da ɗaukakata.
44
“Ta haka zan tsarkake Tentin Sujada da bagaden, in kuma tsarkake Haruna da ’ya’yansa maza su yi mini hidima a matsayin firistoci.
45
Sa’an nan zan zauna a cikin Isra’ilawa, in kuma zama Allahnsu.
46
Za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar saboda in zauna a cikinsu. Ni ne Ubangiji Allahnsu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options