Fitowa 29:26-34
26
Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka.
27
“Ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa, waɗanda za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon naɗin, wanda yake na Haruna da kuma na ’ya’yansa maza.
28
Wannan zai zama rabon Haruna da ’ya’yansa maza daga Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji.
29
“Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na zuriyarsa bayan mutuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su.
30
Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist, shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga Tentin Sujada, don yă yi aiki a Wuri Mai Tsarki.
31
“Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri.
32
A ƙofar Tentin Sujada, Haruna da ’ya’yansa maza za su ci wannan rago da burodin da yake cikin kwandon.
33
Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.
34
In naman ragon naɗi ko wani burodin ya ragu har safiya, a ƙone shi, kada a ci gama tsarkake ne.
Settings