Fitowa 28:1-4
1
“Ka sa a kawo maka Haruna ɗan’uwanka, tare da ’ya’yansa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar daga cikin Isra’ilawa, domin su yi mini hidima a matsayin firistoci.
2
Ka yi tufafi masu tsarki domin ɗan’uwanka Haruna, domin a girmama, a kuma ɗaukaka shi.
3
Ka faɗa wa dukan gwanayen da na ba su hikima a irin abubuwan nan, cewa su yi tufafi saboda Haruna, don a tsarkakewarsa, domin yă yi mini hidima a matsayin firist.
4
Waɗannan su ne tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da efod, da taguwa, da doguwar riga, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan’uwanka, Haruna da ’ya’yansa, waɗannan tsarkaka tufafi, don su zama firistoci masu yi mini hidima.
Settings