Tsallake zuwa abun ciki
Fitowa 25:10-16

Fitowa 25:10-16

10
“Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
11
Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya.
12
Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe.
13
Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.
14
Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa.
15
Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba.
16
Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options