Fitowa 25:10-14
10
“Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.
11
Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya.
12
Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe.
13
Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.
14
Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa.
Settings