Skip to content
Fitowa 21:22-27

Fitowa 21:22-27

22
“Idan mutum biyu suna faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka za a biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara.
23
Amma in akwai rauni mai tsanani, sai a ɗauki rai a maimakon rai,
24
ido don ido, haƙori don haƙori, hannu don hannu, ƙafa don ƙafa,
25
ƙuna don ƙuna, rauni don rauni, ƙujewa don ƙujewa.
26
“In mutum ya bugi bawa ko baiwa a ido, har idon ya lalace, dole yă ’yantar da shi ko ita, maimakon ido.
27
In kuma ya fangare haƙorin bawa ko baiwa, dole yă ’yantar da bawan ko baiwar, a maimakon haƙorin.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options