Fitowa 14:9-12
9
Masarawa, dukan dawakan Fir’auna da kekunan yaƙi da mahaya da sojoji, suka bi Isra’ilawa suka cin musu yayinda suke a sansani kusa da teku kurkusa da Fi Hahirot, wanda ya fuskanci Ba’al-Zafon.
10
Da Fir’auna ya yi kusa, Isra’ilawa suka ɗaga idanu sai suka hange Masarawa daga nesa suna tā da ƙura suna zuwa. Sai suka tsorata ƙwarai, suka kuwa yi kuka ga Ubangiji.
11
Suka ce wa Musa, “Don babu makabarta a Masar ne, ka kawo mu a hamada mu mutu? Me ka yi mana ke nan da ka fitar da mu daga Masar?
12
Ba mu faɗa maka a Masar ba, cewa ‘Ka bar mu mu bauta wa Masarawa’? Ai, da ya fi mana mu bauta wa Masarawa, da a ce mu mutu a hamada!”
Settings