Fitowa 12:1-6
1
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna a Masar,
2
“Wannan wata za tă zama a gare ku wata na farko, wata na fari na shekararku.
3
Ka faɗa wa dukan jama’ar Isra’ila cewa a rana ta goma ga wannan wata, kowane mutum zai ɗauki ɗan rago domin iyalinsa, ɗaya domin kowane gida.
4
In akwai wani gidan da ba za su iya cinye rago guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki rago guda gwargwadon yawansu, bisa ga abin da mutum guda zai ci.
5
Dabbobin da za ku zaɓa, dole su zama bana ɗaya, namiji marar tabo, za ku kuma kamo su daga cikin tumaki ko awaki.
6
Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato, sa’ad da dukan taron jama’ar Isra’ila za su yanka ragunansu da yamma.
Settings