Esta 8:11-13
11
Dokar sarki ta ba wa Yahudawa a kowace birni izini su taru, su kuma kāre kansu, domin su hallaka, su kashe, su kuma hallaka kowace ƙungiyar mayaƙa, na kowace ƙasa, ko lardi, da wataƙila za su kai musu, da matansu, da yaransu hari; su kuma washe mallakar abokan gābansu.
12
Ranar da aka shirya domin Yahudawa su yi wannan a dukan lardunan Sarki Zerzes, ita ce ranar goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato, watan Adar.
13
Za a ba da kofi na rubutacciyar dokar a matsayin ƙa’ida a kowane lardi, a kuma sanar wa mutanen kowace ƙasa, domin Yahudawa su zauna da shiri a ranar, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.
Settings