Esta 1:12-15
12
Amma da masu hidima suka ba da umarnin sarki, sai Sarauniya Bashti ta ƙi zuwa. Wannan ya ɓata wa sarki rai, ya kuma yi fushi ƙwarai.
13
Da yake, al’ada ce sarki yă nemi shawara daga sanannu a batun doka da adalci, sai ya yi magana da masu hikima waɗanda suke fahimtar lokuta
14
suke kuma mafi kusa da sarki. Waɗannan masu hikima kuwa su ne, Karshena, Shetar, Admata, Tarshish, Meres, Marsena da kuma Memukan. Su hakimai bakwai ne na Farisa da Mediya waɗanda suke da dama ta musamman ta kaiwa ga sarki, suke kuma da matsayi mafi girma a masarautar.
15
Ya ce, “Bisa ga doka, me za a yi wa Sarauniya Bashti? Gama ta ƙi yin biyayya da umarnin sarki Zerzes da bābānni suka kai mata?”
Settings