Skip to content
Afisawa 5:3-14

Afisawa 5:3-14

3
Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba.
4
Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.
5
Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.
6
Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.
7
Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
8
Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske
9
(domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya)
10
ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.
11
Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.
12
Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.
13
Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske.
14
Shi ya sa aka ce, “Ka farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options