Afisawa 1:3-5
3
Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.
4
Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa.
5
A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri.
Settings