Mai Hadishi 9:1-6
1
Sai na yi tunani a kan wannan na kuma gane cewa masu adalci da masu hikima da kuma abubuwan da suke yi suna a hannun Allah ne, amma ba wanda ya san ko ƙauna ko ƙiyayya ce take jiransa.
2
Dukansu makomarsu ɗaya ce, masu adalci da masu mugunta, masu kirki da marasa kirki, masu tsabta da marasa tsabta, masu miƙa hadaya da waɗanda ba sa yi. Kamar yadda yake ga mutumin kirki, haka yake ga mai zunubi. Kamar yadda yake ga masu yin rantsuwa, haka ma da masu tsoron yi.
3
Wannan ita ce muguntar da take faruwa a cikin dukan abubuwa a duniya. Ƙaddara ɗaya ce take a kan kowa. Amma zukatan mutane cike suke da mugunta, akwai kuma hauka a zukatansu yayinda suke a raye, bayan haka kuma sai su mutu.
4
Duk wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki!
5
Gama rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba; ba su da wata lada nan gaba an manta da su ke nan gaba ɗaya.
6
Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu, da kuma kishinsu tuni sun ɓace; ba za su taɓa zama sashen wani abin da yake faruwa a duniya ba.
Settings