Mai Hadishi 11:1-3
1
Ka jefa burodinka a bisa ruwaye, gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.
2
Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas, gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.
3
In gizagizai sun cika da ruwa, sukan zub da ruwan sama bisa duniya. Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa, inda ya fāɗi a nan zai kwanta.
Settings