Maimaitawar Shari’a 9:7-12
7
Ku tuna da wannan, kada kuma ku manta yadda kuka tsokane Ubangiji Allahnku, har ya yi fushi a hamada. Daga ranar da kuka bar Masar har sai da kuka isa nan, kuna ta tawaye wa Ubangiji.
8
A Horeb, kun tayar wa Ubangiji har ya yi fushin da ya isa yă hallaka ku.
9
Sa’ad da na hau kan dutse don in karɓi allunan dutse, allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutse yini arba’in da dare arba’in; ban ci abinci ba, ban sha ruwa ba.
10
Ubangiji ya ba ni alluna biyu wanda shi kansa ya yi rubutu da yatsarsa. A kansu akwai dukan umarnan Ubangiji da an furta muku a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar taron jama’a.
11
A ƙarshen yini arba’in da dare arba’in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, allunan alkawari.
12
Sa’an nan Ubangiji ya faɗa mini, “Sauka daga nan da sauri, domin mutanenka waɗanda ka fitar da su daga Masar sun lalace. Sun juye da sauri daga abin da na umarce su, suka kuma yi zubin gunki wa kansu.”
Settings