Maimaitawar Shari’a 9:1-6
1
Ku ji, ya Isra’ila. Kuna gab da haye Urdun, ku shiga, ku kuma kori al’ummai da suka fi ku yawa, suka kuma fi ku ƙarfi, masu manyan biranen da suke da katangar da suka yi tsaye zuwa sama.
2
Mutane ne masu ƙarfi, kuma dogaye, zuriyar Anakawa! Ai, kun ji akan ce, “Wa zai iya tsayayya da Anakawa?”
3
Amma ku zauna da sani a yau, cewa Ubangiji Allahnku, shi ne wanda ya ƙetare ya sha gabanku kamar wuta mai cinyewa. Zai hallaka su, zai rinjaye su a gabanku. Za ku kore su, ku kuma hallaka su nan da nan, yadda Ubangiji ya yi muku alkawari.
4
Bayan Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku, kada ku faɗa a zuciyarku, “Ubangiji ya kawo mu a nan, mu mallaki wannan ƙasa saboda adalcinmu ne.” A’a, saboda muguntar waɗannan al’umma ne ya sa Ubangiji ya kore su a gabanku.
5
Ba domin adalci ko mutuncinku ba ne ya sa za ku mallaki ƙasarsu; sai dai saboda muguntar al’umman nan ne ya sa Ubangiji Allahnku yana korinsu a gabanku don yă cika abin da ya rantse wa kakanninku, wato, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.
6
Ku gane wannan, cewa ba domin adalcinku ba ne ya sa Ubangiji Allahnku yana ba ku wannan ƙasa mai kyau, ku mallaki, gama ku mutane masu taurinkai ne.
Settings