Maimaitawar Shari’a 4:25-28
25
Bayan kun haifi ’ya’ya da jikoki, kuka kuma zauna na dogon lokaci a ƙasar, in har kuka lalace, kuka kuma yi wani irin gunki, kuna aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku, kuna kuma sa shi fushi.
26
Yau, na kira sama da duniya, su zama shaidata a kanku. Idan kuka yi rashin biyayya, lalle za ku hallaka nan da nan daga ƙasar da kuke ƙetare Urdun ku gāda. Ba za ku daɗe a cikinta ba, amma za a kawar da ku ƙaƙaf.
27
Ubangiji zai watsar da ku a cikin mutane, ɗan kaɗan ne kaɗai za su ragu a cikin al’umman da Ubangiji zai kai ku.
28
A can za ku bauta wa allolin da mutum ya yi, na itace da dutse da ba sa gani, ba sa ji, ba sa ci, ba kuma iya sansanawa.
Settings