Skip to content
Maimaitawar Shari’a 3:23-29

Maimaitawar Shari’a 3:23-29

23
A lokacin, na roƙi Ubangiji na ce,
24
“Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka fara nuna wa bawanka ɗaukakarka da ikonka. Akwai wani allah a sama ko a duniya, wanda zai aikata waɗannan manyan ayyukan kamar ka?
25
Ina roƙonka, bari in ƙetare in ga ƙasa mai kyau ɗin nan a ƙetaren Urdun, wannan ƙasar mai kyau ta tuddai, da kuma Lebanon.”
26
Amma saboda ku, Ubangiji ya yi fushi da ni, bai kuwa saurare ni ba. Sai Ubangiji ya ce, “Ya isa haka, kada ka ƙara yin magana da ni game da wannan batu.
27
Haura zuwa ƙwanƙolin Fisga, ka dubi ƙasar da idanunka daga kowane gefe, yamma, da arewa, da kudu, da kuma gabas, gama ba za ka ƙetare wannan Urdun ba.
28
Amma ka umarci Yoshuwa, ka ƙarfafa shi, ka kuma ba shi ƙarfin gwiwa, gama shi ne zai jagoranci wannan mutane su haye, yă kuma ba su gādon ƙasar da za ka gani.”
29
Sai muka zauna a kwari kusa da Bet-Feyor.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options