Maimaitawar Shari’a 26:14-19
14
Ban ci wani daga cikin tsattsarkan rabo yayinda nake makoki, ko in cire wani rabo mai tsarki yayinda nake marar tsarki, ko in miƙa wani sashensa ga matattu ba. Na yi biyayya ga Ubangiji Allahna, na aikata kome da ka umarce ni.
15
Ka duba ƙasa daga sama, mazauninka mai tsarki, ka albarkace mutanenka Isra’ila da kuma ƙasar da ka ba mu kamar yadda ka yi wa kakanninmu alkawari da rantsuwa, ƙasa mai zub da madara da zuma.”
16
Yau Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi waɗannan ƙa’idodi da kuma dokoki, cikin natsuwa ku kiyaye su da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.
17
Kun furta a wannan rana cewa Ubangiji shi ne Allahnku, cewa za ku kuma yi tafiya a hanyoyinsa, cewa za ku kiyaye ƙa’idodinsa, umarnansa da kuma dokokinsa, kuka kuma ce za ku yi masa biyayya.
18
Ubangiji kuwa ya furta a wannan rana cewa ku mutanensa ne, mallakarsa kamar yadda ya yi alkawari, da kuma cewa za ku kiyaye dukan umarnansa.
19
Ya furta cewa zai sa ku zama masu yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al’umman da ya yi. Za ku zama jama’a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku, kamar yadda ya yi alkawari.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings