Skip to content
Maimaitawar Shari’a 20:10-18

Maimaitawar Shari’a 20:10-18

10
Sa’ad da kuka haura don ku fāɗa wa birni, sai ku fara neman garin da salama.
11
In sun yarda da salamar, suka buɗe ƙofofin garinsu, to, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su kuma yi muku aiki.
12
In kuwa suka ƙi salamar, suka fāɗa muku da yaƙi, sai ku yi wa wannan birni ƙawanya.
13
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya ba da shi cikin hannunku, sai ku kashe dukan mazan da suke cikinsa da takobi.
14
Game da mata, yara, dabbobi da kuma sauran abubuwan da suke cikin birnin, za ku iya kwasa waɗannan a matsayin ganima wa kanku. Za ku kuma yi amfani da ganimar da Ubangiji Allahnku ya ba ku daga abokan gābanku.
15
Haka za ku yi da dukan biranen da suke nesa da ku, waɗanda kuma ba na al’ummai da suke kusa ba.
16
Amma fa, a cikin biranen al’ummai da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kada ku bar wani abu mai numfashi da rai.
17
Ku hallaka su ƙaƙaf, wato, Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa, yadda Ubangiji Allahnku ya umarce ku.
18
In ba haka ba, za su koya muku ku bi dukan abubuwan banƙyaman da suke yi, ta yin sujada wa allolinsu, ta haka kuwa ku yi wa Ubangiji Allahnku zunubi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options