Maimaitawar Shari’a 19:15-21
15
Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku.
16
In wani ɗan sharri ya tashi ya yi wa wani sharri, don a sami wani da laifi,
17
dole mutanen nan biyu da suke rikici su tsaya a gaban Ubangiji, a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.
18
Dole alƙalan su yi bincike sosai, in kuma aka tabbatar mai ba da shaida maƙaryaci ne, yana ba da shaidar zur a kan ɗan’uwansa ne,
19
to, sai a yi da shi yadda ya yi niyya yă yi da ɗan’uwansa. Dole ku fid da mugu daga cikinku.
20
Sauran mutane za su ji wannan su kuma ji tsoro, ba kuwa za a ƙara yin irin wannan mugun abu a cikinku ba.
21
Kada ku ji tausayi, rai yă zama a maimakon rai, ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa.
Settings