Maimaitawar Shari’a 18:9-11
9
Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can.
10
Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri,
11
ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.
Settings