Maimaitawar Shari’a 18:1-8
1
Firistocin da suke Lawiyawa, tabbatacce dukan kabilar Lawi, ba za su sami rabo ko gādo tare da Isra’ila ba. Za su yi rayuwa a kan hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta ne, gama wannan ne gādonsu.
2
Ba za su sami gādo a cikin ’yan’uwansu ba; Ubangiji ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.
3
To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa ta bijimi ne, ko ta tunkiya ce; sai su ba firistoci kafaɗar, kumatun, da kuma kayan cikin.
4
Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku.
5
Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su da zuriyarsu daga cikin dukan kabilanku don su tsaya su yi hidima a cikin sunan Ubangiji har abada.
6
Idan Balawe ya tashi daga wani garinku, wurin da yake da zama a Isra’ila, ya tafi a wurin da Ubangiji ya zaɓa, zai iya dawo a duk lokacin da ya ga dama.
7
Zai iya yin hidima a cikin sunan Ubangiji Allahnsa kamar dukan sauran ’yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke hidima a can, a gaban Ubangiji.
8
Zai sami rabo daidai da sauran, ko da yake ya karɓi kuɗin mallaka na iyali da ya sayar.
Settings