Maimaitawar Shari’a 17:2-4
2
In an sami wani namiji ko ta mace mai zama a cikinku, a ɗaya daga biranen da Ubangiji ya ba ku yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku ta wurin karya alkawarinsa,
3
wanda ya saba wa umarnina, har ya yi sujada ga waɗansu alloli, yana rusuna musu, ko ga rana, ko ga wata, ko kuwa ga taurarin sama,
4
in kuwa aka faɗa muku wannan, to, dole a bincika sosai. In kuwa gaskiya ne, aka kuma tabbatar cewa wannan abin ƙyama ya faru a cikin Isra’ila,
Settings