Maimaitawar Shari’a 16:13-17
13
Ku yi shagalin Bikin Tabanakul har kwana bakwai, bayan kuka gama tattara amfanin gona daga masussukarku da kuma daga wuraren matsin inabinku.
14
Ku yi farin ciki a Bikinku, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da Lawiyawa, da baƙi, da marayu, da kuma gwaurayen da suke zama a cikin biranenku.
15
Kwana bakwai za ku yi shagalin Bikin ga Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa. Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan girbinku da kuma cikin dukan aikin hannuwanku, farin cikinku kuwa zai cika.
16
Sau uku a shekara dukan maza su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa; a Bikin Burodi Marar Yisti, da a Bikin Makoni, da kuma a Bikin Tabanakul. Babu wani da zai bayyana a gaban Ubangiji hannu wofi.
17
Dole kowannenku yă kawo kyauta daidai yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace shi.
Settings