Maimaitawar Shari’a 13:5-11
5
Dole a kashe wannan annabi ko mai mafarki, domin ya yi wa’azin tawaye ga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, ya fanshe ku daga ƙasar bauta; gama annabin nan ya yi ƙoƙari yă juye daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, ku bi. Dole ku fid da mugu daga cikinku.
6
In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba,
7
allolin mutanen kewayenku, ko na kusa, ko na nisa, daga wannan ƙarshen ƙasar zuwa wancan),
8
kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi.
9
Dole ka kashe shi. Dole hannunka yă zama na farko a kisansa, sa’an nan hannuwan sauran dukan mutane.
10
Ku jajjefe shi da duwatsu har sai ya mutu, domin ya yi ƙoƙari yă juye ku daga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.
11
Sa’an nan dukan Isra’ila za su ji su kuma tsorata, babu kuma wani a cikinku da zai ƙara yin irin wannan mugun abu.
Settings