Daniyel 9:7-12
7
“Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.
8
Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi.
9
Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;
10
ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba.
11
Dukan Isra’ila sun karya dokokinka suka kuma juya maka baya, sun ƙi yi maka biyayya. “Saboda haka la’anoni da rantsuwar hukunce-hukuncen da suke a rubuce a cikin Dokar Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.
12
Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba.
Settings