Daniyel 4:20-26
20
Itacen da ka gani; wanda ya yi girma da ƙarfe, da tsayinsa ya taɓa sararin sama, wanda ana ganinsa ko’ina a duniya,
21
wanda ganyayensa masu kyau ne yana da ’ya’yan itace da yawa, wanda yake ba da abinci ga duka, yana ba da wurin hutu ga namun jeji, kuma rassansa suna ɗauke da sheƙar tsuntsayen sama.
22
Ya sarki kai ne itacen nan! Ka yi girma da ƙarfi; girmanka kuma ta kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko’ina a duniya.
23
“Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’
24
“Ga fassarar, ya sarki, wannan ita ce doka wadda Mafi Ɗaukaka ya bayar a kan ranka yă daɗe, sarkina.
25
Za a kore ka daga cikin mutane, za ka kuma zauna cikin namun jeji; za ka ci ciyawa kamar shanu, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cif sa’an nan za ka sani cewa Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.
26
Umarni na barin kututturen itacen da saiwoyinsa yana nufin cewa za a maido maka da mulkinka a lokacin da ka gane cewa Mai sama ne yake mulki.
Settings